MAIMAITA TARIHI BOOK 1
Read Online

MAIMAITA TARIHI BOOK 1

1
$3.00

 Farin tawul ta cusa a cikin jakar cikin hanzari sannan ta nufi durowar dake gefen gadonta ta ɗauki kayan ciki masu laushi ta koma gaban jakar ta saka su. Ba ta tsaya daidaita su ba ta wuce gaban madubi ta ɗauki man shafawarta daya, man zaitun, robar zuma, audugar fuska, deodorant, turare, hisnul muslim da man baki.

 Takunta a hanzarce yake lokacin da ta isa cikin sif tsayayye dake ɓangaren ɗakinta na hagu, zanin gado da rigar filo ta dauka guda daya sai rigunan bacci da zani hade da hijabi da setin kayan sakawa guda uku.

 Da ta dawo gaban gadon kallo daya ta yi wa ababen da ta ɗauko ta gamsu ta kammala shirin da ya dace. Cikin hanzari ta saka komai a ƙaramar jakar sannan ta zuge zif. Dai-dai lokacin da aka buɗe ƙofar ɗakin aka sako kai. 

 Da sauri ta juya ta fuskanci ƙofar. Hannunta ne ya tafi bayan wuyanta inda ta murza wajen ta furzar da numfashi.

 "Kin gama?"

Yarinyar da ta shigo mai kimamin kusan shekaru goma sha takwas ta tambaya haɗe da isowa gabanta ta tsaya. Kifta idanu ta yi saboda yanda kamannin yarinyar yayi sak da wanda take shirin shiga huruminsa. Wannan kaɗuwa ya shige cikin daƙiƙai ƙalilan.

 Da sauri Siddiƙah ta gyaɗa mata kai. "Ga shi nan. Kin kammala komai?"

 "Eh, motar na jiranki ta baya." Hannu ta saka ta karɓi jakar hannunta.

 "Kin tabba tar baki bar ƙofar a buɗe ba ko?"

 "Eh, na rufe, ƙofar baya ne kawai a buɗe. Na kashe wutan bayan."

 "CCTƁ?"

 "Na je na duba, na cire baturan." 

 "Yasir fa kin..."  

"Mama, na haɗa komai, yayi bacci. Kiyi sauri kafun wani ya shigo ki tafi. Tun ɗazu motar ta iso. Kar Malam Kabiru ya koma ya gani."

 Siddiƙah ta hadiye yawu sannan ta janyo matashiyar yarinyar ta rungume ta. "Ki kula sosai. Ki tuna duk abun da na fada miki."

 Hannu ta saka ta mayar da silin gashin kalabarta bayan kunnenta sannan ta gyaɗa kanta cikin sauri. “Ban manta ba kun je duba Dada ke da Aunty Salmah, anyi waya jikinta yayi tsanani zaku kwana a Kumo saboda kuna so ku zazzagaya ‘yan uwan da aka kwana biyu ba a hadu dasu ba a can."

 "Rafi'ah kar ki faɗa wa kowa hakan sai wanda ya matsa da son sani ko ya tambaya."

 "Naji Mama, bazan faɗa ba, yallah, imshiy."

 Numfashi ta ja da ƙarfi sannan ta sauke lokacin da idanunta suka kewaye mata ɗakinta watakila a karo na ƙarshe.

 "Idan ya ƙira..." 

 A hankali Rafi'ah ta ajiye jakar hannunta, ta matsa kusa da mahaifiyarta sannan ta riko kafaɗunta. "Mama, kiyi numfashi. Na faɗa miki babu abunda zai faru in sha Allah. I got you covered. A karo na farko ki tafi kiyi son ranki. Ina tare dake indai kin tabba tar abunda kike so kenan."

 Kallon cikin ƙwayar idanunta ta yi wanda suke yi kama sak da na mahaifinta, a ciki babu komai sai tsantsan yaƙeeni na cewar babu abunda zai faru, don haka Siddiƙah ta gyada kanta.

 "Na gode. Da zan turo miki adireshin inda nake amma gudun kar wani ya gani yasa ba zan yi hakan ba. Idan mun gama zan faɗa miki. Sai kuyi ta magana da Aunty Salmah a waya."

 Cikin sauri suka fice daga ɗakin, duka koridon gidan Rafi'ah ta kakkashe wuta cen yanda koda wani zai tashi a bacci ba zai ga gilmawarsu ba. A bude ta samu ƙofar baya ta sulale. Sai da Rafi'ah ta tabba tar Malam Kabiru baya bakin get saboda aikin kwashe ruwa da ta hadashi da shi a kicin din baya sannan suka wuce waje inda motar ke tsaye take jira.

 A karo na farko cikin shekaru ashirin da aure, Siddiƙah ta sa kafa ta fita daga gidan mijinta ba tare da saninsa ba, bare izininsa sannan kuma tare da cikakkiyar niyyar cin amanarsa.

 

 

 


Frequently bought together

© 2026 Azizah Idris Muhammad. All Rights Reserved.

Powered By