
Ko da suka isa Gombe, Tijjani da Sufyaan kai tsaye Hajja Nenne suka nemi gani a falon Ambasada, tunda isarsu basu sameshi a gida ba. Nan ta shigo suka gaisa akayi duk fulatancin da za ayi sannan suka ɗago maganar da ta kawo su.
Sufyaan ne ya fara magana, "Hajja am, mun ji abunda ya faru kuma marar daɗin ji."
"Iyi, haka Allah Yake hukuncinsa ai."
"Da wannan kam Hajja amma yanzu anyi yara anyi jikoki ai koma dai menene sai dai haƙuri a samu a lallaɓa sauran shekarun. Duk da dai bamu san menene ba amma kafun mu samu Yallaɓai muka ga ya dace mu fara samunki, Allah ya huci zuciyarki, mu baki haƙuri ki yafe wannan abun. Saboda gabaki ɗayanmu rayukanmu basu yi daɗi ba da jin wannan batun.
"Amma kiyi haƙuri in sha Allah za a gyara koma menene a tsakani. Ai an girma yanzu kam sai dai mu ku yi mana sulhu ba muji haka a gunku ba kuma."
Kanta na ƙasa tace, "Ku dai yi haƙuri fa kawai, ya riga ya wuce amma ni bazan koma ba."
Tijjani ya kalmashe kafafunsa yace "A'ah, Hajja kar ki ce haka mana, ai babu abunda ya fi ƙarfin Allah idan aka sako Shi cikin al'amura to kuma babu zancen komawa da baya ai."
"Iyi, hukuncin Allah ɗin ake bi ai shi yasa na faɗa muku hakan ai bazan tsaya nayi jayayya daku ba, tunda kuka taso kuka zo musamman na san darajarmu a matsayin iyayenku kuka gani har kuka so yin gyarar, Allah ya baku lada Ya amsa muku kyakkyawar nufinku, amma aurena da Ambasada ai ya ƙare. Wannan na uku ne. Saboda haka babu maganar kome."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Sufyaan ya furta haɗe da shafo fuskarsa, "Amma wannan lallai abu ne na baƙin ciki, Allah Ya sa muku alkhairi a cikin hakan to Ya baku haƙuri da mu gaba ki ɗaya. Shikenan ai, kiyi haƙuri Hajja gaba idan Allah Ya kawo miki wani kamili irinki sai kiyi aurenki."
Murmushi ta yi ɗan guntu, "Alhaji wani aure kuma? Ai sai dai Allah Ya amfana."
Ƙara gode musu ta yi sannan ta shiga cikin gida, inda har yanzu masu koke-koke basu bari ba musamman da ta ke haɗa kayanta zata bar cikin gidan. Ta bayan gidan Ambasada akwai gida a manne nan ya bata yace ta zauna. Yaranta kaf babu wanda yaso amma cikinsu babu mai wadataccen wurin da zai iya sakata a ciki ranar Hashim da Salman sai da sukayi kukan rashin wadata da ba za su iya ɗauke mahaifiyarsu suyi mata muhalli ba.
Amma haka suka karɓi ta yin mahaifinsu, Hajiya Mama ko gezau ana kuka ita kam ko jaje bata yiwa Hajja Nenne ba haka yara suka tayata ƙaura gidan baya. Maƙwabta da yawa idan sun ga Hajja Nenne ce matar da aka saka sai suyi ta kuka suna salati gami da mamakin yanda Ambasada zai iya rabuwa da uwar yaransa matarsa ta farko bayan dattakunsa da kowa yake gani.
A sashen karɓan baƙin Ambasada su Sufyaan suka sameshi bayan sun ci abinci an yi sallah aka sako maganar da ta kawo su. Abun mamaki kawai sai Ambasada yasaka musu kuka, "Allah dai Ya gafarta min saboda na cutar da Hafsatu, na mata cuta iya cutarwa. Mun yi watanni da dama auren da ke tsakaninmu babu shi, amma mun gagara fitowa mu faɗawa duniya cewa aurenmu ya ƙare.
"Babu alaƙar da ta shiga tsakaninmu amma bata fasa hidima da cikin gidana ba haka ta zauna har ta yi watannin nan tun kafun azumin bara. Sai dai zaunar da ita da nayi na hanata tafiya shima cutarwa ne sosai, a haka kuma bata tsira daga tsangwamar abokan zamanta ba.
"Amma ta kai maƙura wannan karon ta nemi na bata 'yancinta. Sai dai Allah Ya yafe min amma kuyi haƙuri. Kuyi haƙuri."
Jikin Sufyaan da Tijjani duk ya mutu murus suka rasa ta inda zasu fara, ƙarshe shima dattijon sai ya koma basu tausayi, shi ya yi abu abun ya dame shi gashi sun gagara fitowa su faɗawa duniya saboda suna shakkan halin da zasu jefa yaransu a ciki, a dalilin hakan kuma sai ƙarin cutar da juna da sukayi.
Jiki babu ƙwari suka ja ƙafafu suka koma inda suka fito, tunda suka fito a falon karɓan baƙin Ambasada kuwa cikinsu babu wanda ya iya cewa komai. Sai daga baya da suka natsa.